Jami’an hukumar Hisbah sun kama tare da ƙona katan na giya 260 a jihar Bauchi

Jami’an Hukumar Hisbah sun kama tare da lalata katan na giya aƙalla 260 a jihar Bauchi

Hukumar Hisbah reshen jihar Bauchi sun kama tare da ƙona aƙalla katan na giya guda 260 a yankin ƙaramar hukumar Misau.

Kwamishinan Hisbah Barrister Aminu Isah ya bayyana haka ga manema labarai a yammacin ranar lahadi

Barrister Aminu Isah ya bayyana sun ɗauki wannan matakin ne saboda su tabbata da hukumar ta cigaba da jajircewa wajan ganin an cigaba da gudanar da dokokin shari’ar addinin musulunci a jihar ba tare da an ci zarafin wani ba sannan ba tare da tsoro ko alfarma ba.

Sannan kwamishinan Hisban ya ƙara da cewa wannan aikin ya gudana ne a gaban jami’an tsaro da kuma shugaban hukumar addinin musulunci ta jihar Bauchi. Barrister Aminu Isah ya sake nanata cewa hukumar Hisbah ta gudanar da wannan aikin nata ne a ƙarƙashin sashe na 403 a kundin dokokin jihar Bauchi wanda ya hana siyar ko amfani da giya a jihar.

Yana ƙara da cewa “Hukumar Hisbah za ta cigaba da jajircewa wajan gudanar da ayyukanta domin ta tabbatar da an cigaba da aiwatar da dokokin addinin musulunci kamar yadda yakamata a duk faɗin jihar.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *