Rahotanni

Jami’an tsaro har yanzu ba su gano wadanda suka jefa min bam a 2014 ba – Buhari ya yi ƙorafi

Spread the love

Da yake bayar da labarin lamarin, Mista Buhari ya ce sna tafiya tare da wasu mutane uku a Kaduna a cikin motar sulke.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koka kan yadda hukumomin tsaro suka kasa bankadowa da hukunta mutanen da suka jefa masa bam a shekarar 2014 a lokacin da yake neman zama shugaban kasa.

Mista Buhari, wanda ya karbi mulki a matsayin shugaban kasa a watan Mayun 2015 kuma shi ne babban kwamandan sojojin kasar tun daga wancan lokacin ya ce, “har yau” ba a jin komai game da maharan.

“Lokacin da na duba sai na ga jini a kan wando da riga na amma babu daya daga cikin mu da ya samu rauni a cikin motar. Amma ko ta yaya, na ga jini saboda yawan mutanen da bam din ya kashe a waje.

“Na fito, na damu da mutanen da suka jikkata. Wasu mutane ne suka tsayar da abin hawa, suka tura ni ciki suka kai ni gida. Karshen sa kenan. Haka jami’an tsaron Najeriya ke da inganci har yau,” in ji Mista Buhari da kakkausar murya.

Shugaban ya tuno da kusan mutuwa a wani shirin fim da aka nuna a gidan Talabijin na Channels a daren Lahadi.

Da yake bayyana lamarin, Mista Buhari ya ce yana cikin mota tare da wasu mutane uku a Kaduna a cikin motar sulke da tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso ya ba shi a lokacin da lamarin ya faru.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button