Jan Hankali Ga Marubutan Yankinmu Na Arewa

Ina mai Jan hankali tare da tunatarwa ga marubutan yankinmu na Arewa dake ta’amuli da kafofin Sadarwar Zamani.

A wannan zamanin babu wata hanya ko kafa da take da tasiri a Duniya da yafi na soshiyal midiya.

Ya kamata duk wani marubuci ya karkato hankalinsa zuwa ga wa yan nan muhimman abubuwan domin amfanan al’ummar yankinsa.

Gasu kamar haka;

1, Mu maida hankali wajan jawo hankalin Gwamnatin Kasar kan matsalar rashin tsaron da ya addabi yankinmu na Arewa.

2, Muji tsoron Allah wajan rubuta gaskiya

3, Mu gujewa yada labarun karya

4, Mu dinga tantance labari kafun yadawa

5, Mu guji cin mutuncin al’umma a kafofin sadarwar zamani

6, Mu maida hankali wajan rubuta abinda zai amfani al’umma

7, Mu maida hankali wajan kare Martabar yankinmu na Arewa

8, Mu maida hankali wajan hada kyakkyawar mu’amala a tsakanin mu.

Na tabbata idan dukkannin marubutan Arewa da gidajen jaridun Arewa suka maida hankali kan wa yan nan muhimman ayyukan zaa samu cigaba mai daurewa a yankinmu na Arewa.

Muna addu’ar Allah ya kawo mana karshen matsalar rashin tsaron da ya addabi yankinmu na Arewa.

Rubutuwa✍🏻✍🏻✍🏻
Comr Abba Sani Pantami
National Chairman
“Arewa Media Writers”.

Daga Comr Abba Sani Pantami

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *