Kasar Amurka ta bada sanarwar tallafin dala miliyan 104 ga Najeriya don magance matsalolin tsaro.

Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) tana ba da kusan dala miliyan 104 don karin taimakon jin kai don magance matsalar da ke faruwa a Najeriya.

Wata sanarwa da hukumar ta U.S. ta fitar ranar Juma’a ta ce kimanin mutane miliyan 8.7 ke cikin hadari.
A cewar sanarwar, wannan karin taimakon zai samar da taimakon da ake bukata cikin gaggawa ga al’ummomi, gami da abinci, kiwon lafiya, abinci mai gina jiki, matsuguni, kariya, ruwa, da tsafta, da kuma shirye-shiryen hada kai.
“Tun daga shekarar 2015, tashin hankali da rashin tsaro sun kori mutane daga gidajensu kuma suka ta’azzara bukatun jin kai a Arewacin Najeriya.

Sanarwar ta ce “annobar corona ta kara yin tasiri ga karancin abinci, ya haifar da damuwar kariya ciki har da barazanar cin zarafin jinsi, da kuma rage hanyoyin samun abubuwan masarufi kamar tsaftataccen ruwan sha, abinci mai gina jiki, da kuma wurin kwana.
Ta kuma kara da cewa Amurka ita ce kasa daya tilo da ta fi bayar da tallafi a Najeriya, saboda ta samar da kusan dala miliyan 505 a cikin Kudin shekarar 2020 da 2021.

“Kasar Amurka na nan kan bakan ta na taimakawa mutanen da wannan rikici ya shafa kuma za ta ci gaba da bayar da muhimmiyar tallafi ga mutanen Nijeriya. Kasar Amurka na kira ga sauran masu hannu da shuni da su yi hakan ta hanyar samar da taimakon ceton rai ga ‘yan Nijeriya masu rauni da kuma sauran al’ummomin.” in ji sanarwar.

Daga Aliyu Adamu Tsiga

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *