Kuyi Kokari Ku Mallaki Katin Zabe, Shawarar Fatima Ganduje Ga Masu Zanga-zangar ENDSARS.

Diyar Gwamna Ganduje ta shawarci masu zanga-zangar #ENDSARS da su mallaki katin zabe.

‘Ya ga gwamnan jihar Kano, Fatima Ganduje Ajimobi ta shawarci masu zanga-zangar #ENDSARS.

Fatima Ajimobi ta shiga shafinta na Instagram inda ta bukaci kowa da kowa ya samu katinsa na zabe ya jefa kuri’a, amma ya tabbata an kirga kuri’un su.

Ta rubuta: “Ku yi zabe kuma kada ku bari sai an kirga kuri’un ku. Bi sakamakon baki daya, ”ta rubuta.

“Mutum ya bibiyi hedkwatar zabe, kuma ya bari ayi ƙidayar kuri’u.

Matasa sune mafiya rinjaye kuma mafi rinjaye mulki shine zai ceci al’ummar mu na Najeriya. #ENDSARS #ENDOPPRESSION # FGA ”ta kara da cewa. A nasa bangaren, mijinta Idris Ajimobi ya bukaci matasa da su shirya katin na su na zabe gabanin zaben 2023.

“Kuna da muryar da ta cancanci a ji saboda haka ku yi amfani da muryarku ta hanyar shirya katin ku na PVC yanzu cikin tsammanin 2023.” ya rubuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.