Rahotanni

Labari Mai Dadin Ji: Ranar Alhamis Mai Zuwa Za A Bude Kasuwanni A Kaduna.

Spread the love

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ranar Alhamis 13/8/2020 za a bude daukacin Kasuwannin jihar.

Sai dai kuma gwamnatin ta ce ya zama wajibi ‘yan Kasuwa su kiyaye dokokin wanke hannu kafin a shiga kasuwar da kuma sanya takun-kumi na rufe baki da hanci.

Kasuwannin jihar Kaduna dai sun kasance a rufe ne tun bayan bullar cutar sarkewar nunfashi ta Covi-19, kuma tun-tuni ‘yan kasuwar sukayita rokon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i da ya bude Kasuwannin amma yaki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button