Rahotanni

Masarautar Zazzau ta kori wani Dogarin fadar saboda ya yiwa wata mata da ke neman taimako wajen Sarkin Zazzau fyaɗe

Spread the love

Majalisar masarautar Zazzau, Kaduna ta ce ta kori daya daga cikin masu gadin fadar ta saboda sun hada kai da abokansa suka yi da wata mata da ke neman taimako wajen Sarkin Zazzau fyaɗe.

A cewar sanarwar da Abdullahi Kwarbai, mai magana da yawun Masarautar Zazzau, ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da matar ta je fadar domin neman ganawa da sarkin.

Kwarbai ya ce mai gadin, Samaila Abubakar, a lokacin da yake yunkurin taimakawa matar, ya kai ta inda ya yi mata fyade tare da abokansa.

Ya ce an sallami wanda ake zargin daga fadar tare da mika shi ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

“Majalisar Masarautar Zazzau karkashin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ta bayar da umarnin korar SAMA’ILA ABUBAKAR RIMIN TSIWA (Daya daga cikin Jami’an tsaron Fadar, Dogari) daga aikin masarautar.” Inji sanarwar.

“Wata mace da ke shirin bikin aurenta da take neman taimako daga Sarki ta tunkari shi (Sama’ila), domin a kai ta gaban sarki amma maimakon ya yi haka, sai ya yaudare ta zuwa wani wuri tare da abokansa inda suka yi mata fyade.

“Majalisar ta umurci ‘yan sanda da su gaggauta gudanar da bincike tare da tabbatar da gurfanar da masu laifin ba tare da bata lokaci ba.”

Majalisar, ta yi alkawarin bin diddigin lamarin tare da tabbatar da samun adalci kan laifin da aka aikata mata.

Thecable

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button