Mata da ƙananan yara ne suka ga bayan Shekau.

Rahotannin da suke shigowa yanzu sun tabbatar da cewa ƙungiyar ƴan ta’adda ta ISWAP tayi amfani da ƙananan yara haɗe da mata ne waɗanda basu wuce shekaru 16 zuwa 30 ba kafin su samu nasarar farma shugaban na Boko Haram Abubakar Shekau wanda tun kwanaki biyu da suke gabata aka sanarda labarin mutuwarsa.

Rahotannin sun ƙara tabbatar da cewa dukkan ɓangarorin biyu sun yi hasarar rayuka duk da cewa ɓangaren da Shekau din yake Jagoranta sun fi rasa mabiya a yayin gwabza yaƙin, wanda a ƙarshe kuma yayi sanadiyar mutuwar Abubakar Shekau kamar yadda ake iƙirari.

Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta bayyana a shafinta; mafi yawancin mayaƙan na ISWAP sun sami horo da ƙwarewar yaƙi na musamman ne daga ƙasashen Libya, Somalia da sauran ƙasashen ƙetare.

Hakazalika, an tabbatar da cewa ɓangaren ƴan ta’addan masu iƙirarin Jihadi na ISWAP dama sun daɗe suna fakon yadda Shugaban na Boko Haram zai shiga hannunsu; wanda a iƙirarin su ya daɗe yana bijirewa tsarukan ƙungiyoyin tare da yin gaban kansa.

Kungiyar ta ISWAP ta zaɓi waɗannan matasa masu ƙarancin shekaru ne bisa ga irin jajircewa da ƙwarewar su a filin Jihadi, kuma mafi yawancin su suna rayuwa ne a gefen tafkin Chadi wurin da tuntuni ya zama tamkar matattarar mayaƙan na ISWAP.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *