Matar Da Mijinta Yayi Mata Saki Uku Saboda Ta Zabi Atiku A 2019 Ta Roki Atiku Da Magoya Bayansa Su Taimaka Mata Da Jari…

Zaben da akayi na shugaban kasa a Najeriya a shekarar 2019 tsakanin shugaban Kasa Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar shine yayi sanadin mutuwar auren Malama Fatima Umar wadda take zaune a jihar Kebbi.

Fatima Umar ta shaidawa jaridar Mikiya cewa tun da farko dama suna da ban-bancin akidar siyasa tsakaninta da Mijinta, domin kuwa shi yana goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, ita kuma tana goyon bayan Alhaji Atiku Abubakar.

Fatima ta ce mijin nata ya yi kokarin hanata zaben Alhaji Atiku Abubakar, amma kuma taki hanuwa, saboda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bata damar zabar wanda ranta yake so, don haka bata ga dalilin da zai sa ya hanata zaben ra’ayinta ba.

Fatima Umar tace bayan ta dawo daga wajen zabe ne sai mijin nata wanda suke da ‘ya’ya Biyar dashi ya saketa saki Uku.

A yanzu haka dai Fatima ita take rike da ‘ya’yan nasu biyar, tun bayan da ya saketa ne ta tattara yaranta ta tafi dasu.

Malama Fatima ta ce ta fara sana’a amma kuma saboda dawainiyar ‘ya’yan nata jarin nata ya karye, shiyasa take rokon Alhaji Atiku Abubakar da daukacin magoya bayansa da su taimaka mata da jari wanda zata cigaba daukar dawainiyar’ya’yanta.

Domin Karin Bayani Sai A Kira Malama Fatima A Wannan Lambar: 07046626023

Leave a Reply

Your email address will not be published.