Matsalar rashin Ruwa a Sokoto: Sanata Wamakko ya dauki nauyin sanar da tankokin ruwa a unguwannin Sokoto.

Sanata Dr Aliyu magatakarda wamakko, mai wakilcin Gundumar sokoto ta tsakiya ya dauki alkawalin cewar,
zai bada cikakkiyar gudunmuwar motocin ruwa ga duk unguwar dake fama da matsalar ruwa a birnin sokoto.

Shirin wamakko na kaiwa unguwanni agajin tankokin motocin ruwa yanzu haka Unguwanni fiye da 50 da masallatan jumu’ah ne suka Amfana kamar yadda shugaban kwamitin bada ruwan
Malam Anas Dan Na Yaba ya bayyana.

Wamakko ya dauki alkawalin cewar, zai cigaba da kaiwa duk wata unguwar dake fama da matsalar ruwa a birnin sokoto.

An shafe watanni 2 kenan ana fama da matsalar ruwan sha a birnin Sokoto, sai dai kuma Gwamnatin jahar ta ce, tana kan aikin ingantawa tare da samar da ingantattun ruwan sha yanzu haka.

Yayin da wasu bayanai suke nuna cewa matsalar bata rasa nasaba da gyaran manyan titunan da Gwamnatin jihar ke yi a halin yanzu ya sanya karancin ruwan duba da yadda manyan bututun ruwan da ke baiwa unguwannanin Cikin jihar ke saman titunan da ake gyara a halin yanzu.

Daga Murtala ST Sokoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *