Rahotanni

Mun kwato dala biliyan 1 da aka sace – Malami

Spread the love

Babban Lauyan Najeriya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa kawo yanzu gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kwato kimanin dala biliyan 1 da aka sace daga shekarar 2015 zuwa 2022.

Malami ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa dake Abuja yayin da yake zantawa da wakilin gidan gwamnati bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako a ranar Laraba.

Ministan shari’a ya ce an tura kadarorin da aka kwato zuwa sassa daban-daban na tattalin arzikin kasar da suka hada da rage radadin talauci.

“Tsakanin 2015 zuwa 2022, gwamnatinmu ta kwato kusan dala biliyan 1 da aka sace daga sassa daban-daban.”

Malami ya kuma bayyana damuwar gwamnati kan al’amuran da suka shafi kasafin kudi, wanda ya bayyana a matsayin abin damuwa, inda ya ce za a binciko duk wani matakin da ya dace don magance shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button