Muna Baiwa Sheikh Pantami Hakuri Kan Rahotan Da Muka Fitar Akanshi, “Cewar Editan Jaridar Independent”

Editan jaridar Independent ya wallafa rubutu tare da bayyana bayar da hakurinsu ga Shehin Malami kuma Ministan Sadarwa Sheikh Dakta Isa Ali Pantami, akan rahotan da jaridar ta fitar.

Yan kwanaki jaridar ta shiga cikin jerin jaridun da suka wallafa labarin cewa kasar Amurka ta sanya malamin cikin jerin masu taimakawa ta’addanci a Najeriya ko kuma nahiyar Afirka baki ɗaya.

Tun bayan wallafa labarin da jaridun sukayi Malamin kuma ministan sadarwa ya ayyana cewa lallai zai maka jaridun a kotu inda yace su shirya magana da lauyoyinsa a kotu tun a ranar.

Jaridar Independent tayi amai ta lashe inda Editan jaridar ya nemi afuwa akan labarin da suka wallafa tare da baiwa Sheikh ɗin hakuri akan abinda labarin nasu ya jawo na cece kuce tare da ɓatawa malamin suna.

Shin ko masu karatu suna ganin ya wannan dambarwar zata ƙare?

Malamin zai haƙura ne ko kuma duk da sun bashi haƙuri zai nemi su biyashi Diyyar ɓata masa suna da sukayi ne?

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *