Rahotanni

Najeriya na asarar gangar danyen mai 700,000 daga barayi kullum – Timipre Sylva

Spread the love

Ministan ya ce satar danyen mai ya yi illa ga shigo da kudaden waje na Najeriya.

Najeriya na asarar akalla gangar danyen mai 700,000 daga barayi a kullum, in ji karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva.

“Satar mai ta hana kasar samun gangar danyen mai kusan 700,000 a kowace rana. Mummunan illar hakan shi ne raguwar samar da danyen mai da raguwar kudaden shiga na kasa,” inji shi.

Mista Sylva ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a wajen bikin yaye daliban Cibiyar Koyar da Man Fetur (PTI) a shekarar 2002 a Effurun, Jihar Delta.

Ministan, wanda ya samu wakilcin Gabriel Aduda, babban sakatare a ma’aikatarsa, ya ce gwamnatin tarayya na kokarin dakile wannan matsala tare da dakatar da mummunan tasirin da Najeriya ke samu a kudaden waje.

Ya ce ma’aikatar man fetur za ta hada kai da majalisar dokokin kasa domin tabbatar da cewa an ba da cikakkiyar kulawa ga gyaran dokar PTI.

Mista Sylva ya ce cibiyar za ta iya samun nasarori sosai idan aka yi wa dokar PTI kwaskwarima domin baiwa cibiyar damar samun karin kudade.

Ya ce ma’aikatar ta bai wa PTI umarni a fannoni daban-daban na bincike kan amfani da kayan cikin gida wajen hako danyen mai, daina harba iskar gas da sayar da iskar gas da dai sauransu.

Ministan ya shawarci PTI da ta rungumi hanyoyin zamani don aiwatar da ayyukanta biyo bayan sauye-sauyen da ake samu a fannin fasaha a duniya da kuma hulda da hukumomin da abin ya shafa na gwamnati da kamfanonin mai na cikin gida da na kasa da kasa.

Mista Sylva ya taya daliban da suka kammala karatun murna tare da ba su tabbacin cewa akwai damammaki a harkar man fetur da iskar gas.

“Kwarewar da kuka samu za su kasance masu mahimmanci wajen tabbatar da ci gaban manufofin da ake samu a masana’antar mai da iskar gas. Ina faɗin haka cikin kwarin gwiwa saboda har yanzu duniya ta dogara da iskar gas,” in ji shi.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button