Rahotanni

Najeriya ta kori ‘yan kasashen waje 70 cikin shekaru biyu – Aregbesola

Spread the love

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Najeriya ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta kori ‘yan kasashen waje 70 cikin shekaru biyu da suka gabata.

An bayyana hakan ne a wata takarda da ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya fitar ranar Juma’a.

Bakin da aka kora bisa laifuka daban-daban, sun hada da mutane daga Jamhuriyar Dimokaradiyyar Koriya, Masar, da Sri Lanka, da dai sauransu.

“A kan umarnin korar da Ministan cikin gida ya bayar a cikin shekaru biyu da suka gabata, Ministan ya bayar da jimillar umarnin korar ‘yan kasashen waje daban-daban guda 70 daga Najeriya saboda wani laifi. Galibin wadanda aka kora sun fito ne daga Jamhuriyar Dimokaradiyyar Jama’ar Koriya, Masar, Sri Lanka, da sauran wasu da dama,” in ji sanarwar.

Ministan ya ci gaba da cewa, an kammala shirye-shiryen kafa Cibiyar Kula da Tsaron Cikin Gida don inganta tsaron cikin gida na kasar nan.

Ya kara da cewa, an tanadi fili mai fadin hekta 45 a garin Ilesa na jihar Osun domin kaddamar da cibiyar.

Ya ce rashin samun irin wannan cibiya ya haifar da gagarumin gibi a bangaren jami’an tsaro da sauran hukumomin tsaro a kasar nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button