Rahotanni

Rikicin Obajana: Mun bankado shirin Dangote na tada zaune tsaye a jihar Kogi – Gwamna Yahaya Bello

Spread the love

Gwamnatin Kogi da kuma hukumomin Dangote Cement Plc. suna takun saka a kan mallakar kamfani.

Rufe kamfanin na wucin gadi da wasu matasa suka yi a baya ya haifar da cece-kuce tsakanin gwamnatin jihar da kamfanin da ke Obajana, kusa da Lokoja.

A ranar Asabar ne gwamnatin jihar ta yi zargin cewa mahukuntan kamfanin na shirin kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.

Gwamnatin jihar a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kingsley Fanwo ya fitar a Lokoja, ta ce gwamnati na da hujjoji da ke tabbatar da zargin da ake yi mata.

“Mun bankado wasu tsare-tsare da kamfanin ya yi a wani taro da aka gudanar a daren jiya na haifar da hargitsi a fadin jihar a matsayin dabarun yaki da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na samun nata daidaiton tallafin da ta dace daga kamfanin siminti,” in ji kwamishinan.

Kwamishinan ya kuma yi zargin cewa mahukuntan kamfanin sun yi niyyar hada wasu hanyoyin tsaro domin muzgunawa wasu jami’an gwamnati.

“Sun yanke shawarar toshe dukkanin manyan titunan jihar da manyan motocinsu ke bi domin hana zirga-zirga a jihar.

“Idan kamfanin ya yi ƙoƙarin aiwatar da duk wata barazanarsa ko kuma musanta ikirarinmu wanda hujjoji ke goyan bayan, za mu fitar da bidiyo da sautin taron nasu kan wannan,” in ji Mista Fanwo.

Daya daga cikin jami’an hulda da jama’a na kamfanin, Abubakar Jibrin, ya ce ba zai ce uffan ba kan duk wani batu da ya shafi lamarin.

Amma hukumomin Dangote Cement Plc. sun ce gwamnatin jihar ta yi amfani da wasu gungun mutane wajen lalata kadarorin kamfanin tare da raunata wasu ma’aikatan.

A wata sanarwa da Sashen Sadarwa na Kamfanin Dangote Cement Plc ya fitar. a Lokoja, mahukuntan kamfanin sun yi zargin cewa wasu mutane ne suka kai farmaki gidan simintin a ranar Laraba.

“A kasa da ma’aikatan kamfanin 27 ne ke cikin mummunan yanayi a halin yanzu bayan mamayewar.

“An kuma kona motocin dakon siminti, an kuma kona wasu da dama, yayin da suka dauki bas din kamfanin da karfin tsiya.

Sanarwar ta ce “Tun bayan harin, an kai wa motocinmu dauke da dizal hari a hanyar Anyigba.”

Sanarwar ta ce a halin yanzu an kwantar da wasu wadanda harin ya rutsa da su a sashin gaggawa na asibitin kwararru na jihar Kogi da ke Lokoja.

NAN

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button