
RUWA KAMAR DA BAKIN KWARYA….

Yadda ruwan sama ya yiwa garin Doko dake ƙaramar hukumar Garki jihar Jigawa ƙawanya wanda sanadiyar hakan wasu suka rasa matsugunnansu sannan ya mamaye gonakan manoma da yawa.

Tabbas tunda nake ban taɓa ganin ruwan sama kamar na yau ba. Wannan ya tuno mini da alkhairin da tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Ibrahim Saminu Turaki ya yi mana na haƙa mana magudanar ruwa da kwalbatoci a cikin gari, banda haka, da abin yafi haka muni.
Amma duk da haka har yanzu muna buƙatar a ƙara haƙa mana manyan kwalbatoci a cikin gari. Bisa wannan, muke roƙon masu ruwa da tsaki a cikin gwamnatin dasu dubi kokenmu da idon basira domin ceto ɗaruruwan magidanta daga rasa muhallansu da kuma kange wasu ɗaruruwan manoma daga asarar amfanin gonar da suka shuka.
Daga Mutawakkil Gambo Doko