Sarki Muhammadu Sunusi II zai jagoranci sallar idi a Kaduna

Bana a Kaduna Sarki Muhammadu Sanusi II zai jagoranci sallar idi

Rahotanni daga jihar Kaduna suna bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa ko ma sun kammala inda ake sa ran mai martaba tsohon Sarkin Kano kana sabon Khalifa a Faidah Tijjaniyya Muhammadu Sanusi II shine zai jagoranci sallar idi a wani masallacin idi.

Jaridar Manuniya ta ruwaito tuni ana ta kammala gyara filin idin da Sarkin zai jagoranci sallar.
“Yanzu haka muna wajen kuma muna ta karasa yan gyare-gyare domin shirin idi a gobe Alhamis in sha Allahu” a cewar wata majiya da ta nemi a sakaye sunan ta.

Sai dai babu wata sanarwa a hukumance kan batun sannan duk kokarin da Manuniya tayi na jin bakin babbar hadimarsa Saadatu Baba Ahmad abun ya faskara domin taki amsa waya sannan taki maido da sakon tes da wakilin Manuniya ya tura mata domin ta tabbatar da labarin.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *