Shugabannin Izala Ne Yakamata Su Fito Su Fadawa Buhari Gaskiya, Inji Aisha Usman Golden.

Malama Aisha Usman ta kala-balanci shugabanni Ƙungiyar Izala akan fadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari gaskiya saboda irin rawar da suka taka wajen yakin neman zabe.

Tace “Shugabannin Izala kune kukayi ruwa da tsaki a hudubobinku da guraren wa’azinku cewa azabi Buhari shine me gaskiya, shi ze fidda talaka daga halin kuncin da a wancan lokacin muke ganin talaka na ciki, harma kuke kokarin nuna cewa Wanda be zabeshi ba ya kafirta.

“To yau gashi talaka ya wayi gari a hali mafi kunci Wanda ya ninka kuncin da a wancan lokacin yake ciki sau ba adadi, dan haka ya zama hakki akanku yadda kukayi kira azabeshi haka zaku fito kuyi kira da ya sauya salon milkinsa ya lalubo hanyar da ze sassautawa talakawa.”

Ta Kara da cewa “shinkafa#1300 ,1500,1700 mudu , biskin masara #800,900, mudu, Ina talaka zesakansa ?

“Ta inda akahau tanan ake sauka, dan haka kuyi dik me yiwuwa wajen fadakar dashi halin da talaka ke ciki wata kila dan darajar addini ku din zai saurareku yayi amfani da maganarku.”

“Idan kuwa kukayi shiru kuka kama bakinku to ba makawa idan kukaje lahira Allah sai ya tambayeku” Inji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.