Ta so ta damfareni maƙudan kuɗaɗe ne, ni kuma sai naƙi, in ji Aliko Dangote.

Attajiri Aliko Dangote ya bukaci wata kotu dake Amurka da ta shiga tsakanin sa da tsofuwar budurwar sa Autumn Spikes wacce yanzu haka ke amfani da kafafen sadarwa tare da wallafa wasu daga cikin hotunan ta tare da Aliko Dangote.

Autumn Spikes Wannan mata ta bayyana cewa sun share kusan shekaru 10 tare da Aliko Dangote a matsayin budurwarsa.

A wani labarin da wannan mata ta wallafa wani bidiyon ta tare da attajirin Aliko Dangote,sai yanzu haka Dangote ya bayyana cewa ta yi kokarin danfarar sa milyan biyar na dallar kudin Amurka, ta kuma yi amfani da haka cewa in dai har ba ta samu biyan bukata ba za ta wallafa wasu daga cikin hotunan da sukayi tare.

Autumn Spikes ta ce za ta bi hanyoyin da suka dace don kwato hakkokin ta kamar dai yadda dokokin kasar da suke ciki suka shimfuda.

Spikes ta ce Attajirin ya yi mata tayin kudi da nufin ta rufe maganar alakarsu.

Kallo ya koma bangaren kotu yanzu haka, inda ake sa ran za su bayyana 9 ga watan Fabarairu shekarar 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *