Rahotanni

Tashin Hankali: Ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da gawarwaki dari biyar a jihar Neja

Spread the love

Al’ummar garin Mariga da ke karamar hukumar Bariga a jihar Neja na neman gawarwaki fiye da 500 da ake zargin ambaliyar ruwa ta tafi da su.

Babban limamin masallacin Mariga, Alhassan Na’ibi ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

“Yanzu muna neman gawarwaki sama da 500 da aka binne a makabarta a garin Mariga wadanda muka yi imanin cewa ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da su a Mariga,” in ji babban limamin.

Mista Nai’bi ya kuma kara da cewa al’ummar yankin sun rude domin sun kwashe wasu gawarwaki kimanin 100 daga makabartar zuwa wani wurin binnewa don hana ambaliyar ruwa ta kwashe su.

Babban limamin, wanda ya danganta matsalar da ayyukan masu hakar ma’adanai da ke kusa da makabarta, ya koka da cewa ba su taba samun irin wannan yanayin ba sama da shekaru 60 na makabartar.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin Neja da ta gaggauta kawo musu dauki.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button