Rahotanni

Tinubu ya karyata jita-jitar mutuwarsa, ya wallafa bidiyonsa yana motsa jiki

Spread the love

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya bayyana cewa yana da karfi kuma yana cikin koshin lafiya yayin da ya yi watsi da rade-radin cewa ya mutu.

Tsohon gwamnan jihar Legas, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, ya kuma yi watsi da ikirarin cewa ya janye daga takarar shugaban kasa a 2023.

Tweet ɗin ya kasance tare da faifan bidiyo da ke nuna shi yana aiki akan keken motsa jiki.

Ya rubuta, “Da yawa sun ce na mutu; wasu kuma na cewa na janye daga yakin neman zaben shugaban kasa. To… a’a.

“Wannan ita ce gaskiyar: Ina da ƙarfi, ina cikin koshin lafiya kuma a shirye nake in bauta wa ‘yan Najeriya tun daga rana ta ɗaya.”

An nuna damuwa game da halin da Tinubu yake ciki bayan ya kasa fitowa kan yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan takarar shugaban kasa suka rattabawa hannu a zaben 2023 mai zuwa.

Sai dai ya samu wakilcin mataimakinsa kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a wajen taron.

Da yake bayar da dalilan rashin halartar dan takarar jam’iyyar APC, dan majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar, Ayo Oyalowo, ya bayyana cewa Tinubu ya tafi Landan ne domin ya huta.

Sai dai babu tabbas ko faifan bidiyon da dan takarar shugaban kasa ya raba a shafin Twitter an dauki shi a Landan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button