Tuna Baya: Ban Yarda Da Najeriya A Matsayin Dunkulalliyar Kasa Ba~ Bola Tinubu.

Wata magana kenan da Bola Ahmed Tinubu ya taba faɗa a jaridar Sunday Politics, wadda yake nuna cewa bai yarda da Najeriya a matsayin dunƙulalliyar ƙasa ba.

Yanzu haka dai alamu sun nuna cewa Chief Bola Ahmad Tinubu yana neman takarar kujerar shugaban a ƙarƙashin jam’iyyar APC, sai dai kuma ita wannan maganar da ya taba yi a jaridar Sunday Politics ta fara bazuwa a shafikan yanar gizo, wanda hakan zai iya bashi matsala a kokarinsa na zama shugaban Kasar Najeriya.

So tari ‘yan siyasa sukanyi wasu magan-ganu ba tare da tunanin abin da zai faru a gaba ba, wanda hakan yake baiwa ‘yan adawarsu damar yin kakkausar suka game da kalaman nasu.

Daga Mutawakkil Gambo Doko.

Leave a Reply

Your email address will not be published.