Wani Dattijo ya bawa Shugaba Buhari shawarar ya karo Aure ko tunanin sa zai dawo.

Wani Dattijo mai suna Iliyasu Garba ya bawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari Shawarar ya samo wata tsaleliyar budurwa ya aura ko hankalinsa da tunanin sa zasu dawo.

Dattijon mai suna Iliyasu Garba ya bayyana cewa zama da mace daya zuwa wani tsahon lokaci na jawowa mutum ya samu matsala harya kasa gane abubuwa da dama.

Saboda haka Dattijon yace duba ga yadda abubuwa suka rikicewa Shugaba Buhari kuma yakasa gano kansu to yana Shawartar sa da ya karo Aure yadaure yasamu wata tsaleliyar budurwa ya Aure kafin wa’adin mulkin sa ya kare.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *