Wani Fasto dan jihar Filato da ya bace ya fito a sabon bidiyon Boko Haram, ya nemi Gwamnatin Najeriya ta cece su shi da Mata Biyu Ciristoci da suke tsare.

Wani malamin Cocin Christ in Nations, Jos, Jihar Filato, wanda aka fi sani da Reverend Polycap Zango, wanda ya bata lokacin da yake tafiya zuwa Jihar Gombe don wani taro, ya bayyana a cikin wani sabon bidiyo yana mai cewa kungiyar Islamic State West Africa Lardin ta sace shi.

Zango ya ce yana hannun masu tayar da kayar bayan tare da wasu mata Kirista guda biyu, wadanda su ma aka sace.

A cikin bidiyon, an ga malamin yana zaune yana cewa an sace shi a ranar Litinin, Oktoba 2020.

Ya ce, “Sunana Reverend Polycap Zango kuma ni fasto ne a COCIN LCC Wild Life Park, Jihar Filato, Najeriya.

“A ranar 19 ga Oktoba, 2020, na yi tafiya zuwa wani taro a Gombe lokacin da’ yan kungiyar Boko Haram suka sace ni suka kama ni a hanya.

“A yanzu haka ina tare da su. “Ina kira ga gwamnan jihar Filato, Simon Boko Lalong, da sanatan Filato ta Arewa, Barista ID Gyang, da kungiyar Kiristocin Najeriya da COCIN don Allah su taimaka su cece ni daga hannunsu.

“Sun kuma sace wasu mata Kirista guda biyu wadanda su ma suna nan tare da ni, muna rokon a kubutar da mu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.