Wasu ƙasashe guda bakwai bayan Najeriya, da suka dakatar ko haramta twitter a duniya

Ƙasashen Da Suka Haramta Ko Dakatar Da Manhajar Twitter A Duniya
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da amfani da twitter a ƙasar, kamar yadda ministan yaɗa labaran ƙasar Alhaji Lai Mohammed ya bada sanarwa a yammacin ranar Juma’a.
Wannan matakin yana zuwa ne bayan da shafin na twitter ya goge bayanin shugaba Muhammadu Buhari ya yi wanda ya gargaɗi masu ƙoƙarin tada zaune tsaye a ƙasar.
Dan haka, jaridar MIKIYA ta tattara ƙasashen da suka dakatar da twitter ko suka haramta ta kwata-kwata a duniya:
1- China
A hukumance, an dakatar shafin twitter a China, mafiya yawan ƴan china suna tafiya gaban ofishin jakadancin ƙasar domin su yi amfani da manhajar. Sannan kamfanoni a ƙasar da hanyoyin sadarwa mallakin china kamar Huawei da CCTV suna amfani da twitter bayan gwamnati ta amince musu
China ta dakatar da twitter a shekarar 2009 bayan zanga-zanga wacce ta faru a arewa maso yamma a yankin Xinjiang, wacce ta haddasa tahintahina tsakanin musulman Uyghur da hukumomin ƙasar China. Kamar yadda wasu rahotanni suka rawaito, musulman waɗanda su ne masu ƙaranci a yankin suna amfani da twitter da facebook wajan tattauna yadda za su shirya zanga-zangar tawaye a yankin
2- Egypt
An dakatar da manhajar Twitter a Masar a ranar 25 ga watan Janairu, 2011 a loƙacin da aka gudanar da zanga-zanga a ƙasar.
Bayan sati ɗaya, aka ɗage haramcin.
3- Uganda
A watan Janairu 2012, hukumar sadarwa ta ƙasar Uganda ta bada dokar dakatar da duk wasu hanyoyin isar da saƙo ta yanar gizo-gizo da shafukan sada zumuntar zamani, har sai an bada umarnin ɗage haramcin.
4- Iran
A shekarar 2009 a loƙacin zaɓen shugaban ƙasar Iran, gwamnatin ƙasar ta dakatar da shafin twitter a ƙasar saboda tsoron gudanar da zanga-zanga wacce ake zargin an shiryata a shafin na twitter
A watan Satumba na shekarar aka ɗage haramcin amfani da shafukan sada zumuntar facebook da twitter sakamakon samun tagarɗar na’ura, amma cikin ƴan kwanaki aka sake rufe shafukan.
5- Koriya Ta Arewa
A watan Afrilu 2016. Ƙasar Koriya ta Arewa ta dakatar da amfani da shafin twitter a ƙasar. Duk wanda ya yi yunƙurin amfani da manhajar ba tare da samun izni daga wurin gwamnati ba walau ɗan ƙasar ko kuma wanda ya je da niyyar ziyara zai fuskanci hukunci mai tsanani
6- Turkey
A ranar 21 ga watan Mayu 2014, Ƙasar Turkey ta haramta amfani da manhajar twitter na wucin-gadi, bayan da kotu ta bada umarnin dakatar da shafin. Wannan ya biyo bayan furucin da firayiministan ƙasar Tayyib Erdogan ya yi na “a kori twitter”
7- Turkmenistan
A shekarar 2018, Jaridun ƙasashen ƙetare da shafukan yanar gizo-gizo da kuma shafuka sada zumuntar zamani kamar twitter aka dakatar da su a ƙasar Turkmenistan
Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *