Wasu Bayanai Game Da Rayuwar Hajiya Dada, Mahaifiyar Su ‘Yar Adua.

Hajiya Dada ita ce Mahaifiyar tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa ‘Yar Adua, kuma har yanzu tana nan da ranta, ga wasu bayanai game da rayuwarta.

Mijinta Musa ‘Yar’Adua tsohon minista ne, sannan kuma ita ta haifi tsohon mataimakin shugaban kasa a 1979- 1981, wato marigayi Shehu Musa ‘Yar’adua.

Haka kuma ita ce mahaifiyar gwamnan da ya yi shekara takwas a jihar Katsina (Umaru Musa ‘Yar’Adua) 1999 -2007 daga bisani ya zama shugaban kasa daga shekarar 2007-2009.

Haka kuma jikanta, ya yi minista a 2009-2011.

Sannan kuma jikokinta mata guda uku suna auren tsoffin gwamnoni a kasar nan, wato na Kebbi, Bauchi da Katsina.

Allah ya karawa Hajiya Dada nisan kwana mai albarka. Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *