Wauta ce Gwamnan Adamawa ya yi na barazanar rushe Gidanjen mutane Saboda Fakitin Indomie, martanin Shehu Sani ga gwamna Fintiri.

Sanata Shehu Sani ya yi raddi ga gwamnan jihar Adamawa akan kalamansa da yayi na barazanar rushe gidan da aka sami kayan tallafin Covi-19 da aka sace a jihar a makon da ya gabata.

Shehu sani a shafinsa na Twitter ya yi Allah wadai da sanarwar da aka ce gwamnan na Adamawa ya yi.

Sanata Shehu Sani ya ce wauta ce sosai ga gwamnan jihar Adamawa ya yi barazanar rusa gidaje saboda fakitin indomie.

Ga maganar Sanata Shehu Sani cikakke kamar yadda aka tabbatar da shi daga shafinsa na Twitter, bayan ya yi Tweet;

“‘Wauta ce ga Gwamnan Adamawa ya yi barazanar rusa gidaje saboda fakitin Indomie’.

Tuni jama’a suka yita maida martani game da sakon na Sanata Shehu Sani, inda wasu ke nuna goyon baya, wasu kuma suna kalubalantar sakon nashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.