Yan shi’a sunyi ranstsuwa cewa bazasu taba daina zanga zanga domin a saki Zakzaky ba. Sunce yan’ sanda sun turasawa wa Matan shi’a da ke cikin hijabbansu.


A ranar litinin a Abuja, yan sanda sun sukar wa yan’ Shi’a tiyagas tare da kai masu farmaki a lokacin da suka fito zanga zanga suna mai cewa lallai sai an saki shugabansu.

Wannan zanga zangar wadda aka gudanar a yankin Wuse a inda yan sanda suka rushe ta a kasuwar Wuse ta hanyar sakin tiyagas da kora su daga wurin.

An fadi cewar yan sanda sun turasa matan da suka fito wannan zanga zanga a inda suka dake su harda cire masu hijabbai kuma suka jiwa dayawa daga cikinsu ciwo.

Sakataren wannan zuga, Abdullahi Musa shine ya tabbatar da wannan al’amari kuma yace bazasu taba daina gwagwarmaya domin a fiddo masu da shugabansu ba, saidai yan sandan suyi duk abinda zasuyi.

“Yace, “Yan sanda sun azabtar da mutanen mu da yawa wurin wannan zanga zangar wadda mukeyi cikin lumana inda har suka cirewa mata hijabi.

“Bamuyi dogaro da kowa ba sai Allah, kuma duk yadda za a azabtar da mu bazamu taba yin watsi da shugaban mu ba kuma zamu cigaba da gwagwarmaya har sai an bashi ‘yancin sa daga tsare shi da akayi ba a kan gaskiya ba.

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *