Yanzu haka wani tsohon shugaban kasa Yana shirya makarkashiya domin a tunbuke shugaba Buhari daga Mulki – BMO.

Kungiyar Buhari media organization (BMO) ta zargi wani tsohon Shugaba a Najeriya da shirya makarkashiyar tunbuke Gwamnatin Shugaba Buhari.

Kungiyar ta ce tsohon Shugaban ya hada kan wasu fitattun mutane a Najeriya don tada zaune tsaye, wanda hakan zai iya kawo sanadin kifar da Gwamnatin Buhari.

Saidai kungiyar bata ambaci sunan tsohon Shugaban kai tsaye ba, lamarin da ya jawo ake zargin chief Olusegun Obansanjo ne take nufi, wanda hakan ya jawo cece kuce a tsakanin manyan ‘yan siyasar kasar.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *