Rahotanni

Za mu samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya miliyan 21 nan da shekarar 2025 – Gwamnatin Buhari

Spread the love

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ce ta kuduri aniyar samar da yanayin samar da ayyukan yi miliyan 21 da kuma fitar da mutane miliyan 35 daga kangin talauci nan da shekarar 2025.

Ministan Kwadago Chris Ngige ne ya bayyana hakan a yayin wani taron horas da ma’aikatu kan inganta samar da ayyukan yi a ranar Juma’a a Abuja, kamar yadda wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar.

Ministan ya ce ba za a iya yin watsi da yawan marasa aikin yi a kasar ba.

“Ma’aikatar tare da hadin gwiwar abokan zamanta da masu ruwa da tsaki, sun dauki matakai na gaggawa wajen samar da ayyukan yi, karfafawa matasa gwiwa, da kuma kara yawan aiki,” in ji Mista Ngige.

Ministan ya yi fatan taron zai taimaka wajen bin hanyoyin da za a bi don samar da ayyukan yi.

“Irin wadannan ayyuka masu daukar hankali wadanda za su karfafa samar da ayyukan yi mai dorewa sun hada da karfafa tsarin kasuwanci tun daga matakin farko don cusa al’adun sana’o’in dogaro da kai a tsakanin yara a matakin farko,” in ji shi. “Sauran kuma suna samar da wuraren rance a farashi mai rahusa, wanda zai karfafa wa matasa gwiwa su shiga harkar kasuwancin noma, tare da inganta tsarin injiniyoyi, aikin gona.”

Ministan Kwadago Ngige ya kuma bayyana wasu hanyoyin da za a bi wajen samar da karin guraben ayyukan yi a birane da karkara ta hanyar karfafa yawon bude ido da samar da ababen more rayuwa musamman wutar lantarki da hanyoyin sadarwa masu kyau.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button