Zafafan Tambayoyi Guda 7 Da Injiniya Yakub Umar Ibrahim Ya Akawa Da Shugaba Buhari.

1- Wai don Allah don Annabi shugaba Buhari daman baka da wani kyakykyawan tsari da manufofi na cigaban kasarnan, tsahon shekaru 12 daka kwashe kanaiwa talakawan Najeriya romon baka?

2-Wai dama shugaba Buhari bakasan yadda ake tafi da jagorancin Al’umma ba duk da tarin mukaman daka rike a baya.?

3- Wai shin don Allah shugaba Buhari da gaske tun asali kana kishi da tausayin talakan Najeriya kuwa ?

4- Maigirma shugaban mu kodai ka mance menene primary responsibility na shugabanni akan al’ummar su?

5- Shin Baba ba kaine kace mana idan muka karayin kuskuren sake zabar jam’iyar PDP na shekara 4 sai munkai yanayin in mun ganka bazamu gane ka ba, kuma kaima bazaka ganemu ba.

6- Baba harna tuno lokacin da kake kuka a shekarar 2011 saboda karasa damar dazaka taimake mu, shin dama ba don mu kake kukan ba.?

7- Dana tuno ba a dawwama a duniya se tausayinka ya kamani.

Ko ka manta da makusantanka Abba Kyari da Isma’il Isah Funtua duk Allah ya karbe abinsa.?

Sannan anya baba kasan halin tsanani da al’ummarka suke ciki, shin anya kuwa Baba kana samun bayanan fatara da yunwa dake neman kassara jama’arka?

Inji engr yakub Umar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.