Zan yi sallar Idi a Abuja, ba na bukatar wani yakawomin ziyarar sallah, kowa ya zauna a gida, in ji shugaba Buhari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa zai yi sallar idin sa a fadar shugaban ƙasa dake Aso-rock Abuja.

Ya bukaci Shugabannin Addinai, al’umma da na yankuna da suyi zaman su ba sai sun kai masa wata ziyarar gaisuwar sallah ba.

Ya ce ya yanke Shawarar yin hakan ne sakamakon muguwar annobar Corona da ta zama ruwan dare game Duniya.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *