Tsaro
RAHOTO:-Matsalar Tsaro A Zamfara: An sace Mutane 25.
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Rahoton dake fitowa yanzu daga Zamfara ya Nuna Yan Bindiga sun shiga garin Bindin dake karamar Hukumar Maru ta Jahar Zamfara.
Maharan Sun Rufe hanyar shiga garin Inda Suke bi Gida Gida suna Daukar mutane Sun Tsere da mutane akalla 25 Suka shiga JeJi dasu Sai dai sun sako wata mata da suka Fahimci tana Shayar da Jariri Sannan Mutum 1 Ya kubuta Hannunsu Shi yake Bada Labarin Sako Matar mai Shayar wa.
Idan Buku mantaba Kuma a yau ne Kungiyar matasan Arewa ke Gudanar da Zanga Zangar Rashin Tsaro a Jahar Katsina Jahar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Yafito.
Allah ya Kawo mana Mafita.