Labarai

Ramadan: Marwa ya bukaci Musulmin Nageriya da su yi wa Tinubu da gwamnoni addu’a

Spread the love

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya bukaci ‘yan Najeriya musamman musulmi da su yi wa shugaban kasa Bola Tinubu da sauran jami’an gwamnati addu’a a lokacin azumin watan Ramadan.

A wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Litinin, ya bukaci Musulmi da su yi addu’a ga Tinubu, gwamnonin jihohi, ministoci, da sauran jiga-jigan ‘yan siyasa a cikin kasar nan da addu’ar Allah ya ba su lafiya a cikin watan Ramadan.

Marwa ya bayar da wannan bukata ne a jawabinsa a Masallacin Jumat na tunawa da Alhaji Mohammed Lawal da ke Asokoro, Abuja, lakca kafin Ramadan a ranar Lahadi, 3 ga Maris, 2024.

A cewarsa, a kalandar Musulunci, watan Ramadan ya kebanta da shi, domin a lokacin ne aka saukar da Alkur’ani mai girma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button