Rahotanni
Ranar Ma’aikata: Kungiyar Kwadago Ta Yi Kira Da A Gaggauta Biyan Mafi Karancin Albashi

Daga Haidar H Hasheem Kano
A ranar ma’aikata data gudana a jiya 1 ga watan Mayun 2020, kungiyar kwadago tayi kira da kakkausar murya akan a biya ma’aikata mafi karncin albashi.
Yayin da ake gudanar da taron a wasu sassan jahohin Najeriya a jiya Kungiyar tayi kiranne a babban ofishinta dake Abuja a jiya.
Cikin jawabin sun aiyana cewa wannan tsarin na Mafi karancin albashi shine 30,000 ga karamin ma’aikaci, inda suka baiyana yin hakan a matsayin umarnin shugaban kasa.
Kungiyar ta yan Kwadago sunyi kira ga dukkan Gwamnonin Najeriya dasuyi kokarin fara biyan wannan kudaden ga ma’aikata baki daya.