Labarai

Kwankwaso kokarin Chanja kundin tsarin jam’iyar NNPP ciki harda logon jam’iyar.

Spread the love

Bangaren Sanata Rabi’u Kwankwaso na NNPP ya yi yunkurin yiwa kundin tsarin mulkin jam’iyyar kwaskwarima da tambarin jam’iyyar.

Adita na kasa na NNPP, Ladipo Johnson, ya tabbatar da yin kwaskwarima ga kundin tsarin jam’iyar.

Wannan ci gaban dai na zuwa ne kwanaki uku bayan da bangaren jam’iyyar a karkashin jagorancin Manjo Agbo suka kori Kwankwaso bisa zargin cin hanci da rashawa da kuma karkatar da kudaden yakin neman zaben jam’iyyar.

Yunkurin da sansanin Kwankwaso ya yi na gyara tambari da kundin tsarin mulkin shi ne don rage karfin guiwar wanda ya kafa jam’iyyar NNPP, Dokta Boniface Aniebonam Johnson ya ce. Wani abu ne da muka riga muka tattauna a NEC. Ba kamar su (bangaren Agbo) ba, mu mutane ne na gaske. Amma har yanzu ba mu canza tambarin ba tukuna. Muna shirin jefa shi a cikin ra’ayoyin mambobinmu domin suyi muhawara su fito da tunani. “

Mukaddashin shugaban kungiyar na kasa, Manjo Agbo, ya ce suna sane da matakin da suka dauka na dabara, wanda suke ganin an yi shi ne domin cire riga-kafin wanda ya assasa jam’iyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button