Rashin hankali ne ƴan fashi suka sace sama da ɗaliban makarantar sakandare 600 a lokacin ziyarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a jihar Katsina, in ji Aare Onakakanfo na kasar Yarbawa Gani Adams.
Gani Adams ya mayar da martani game da sace ɗalibai a Kankara.
Aare Onakakanfo na kasar Yarbawa, Iba Gani Adams, ya mayar da martani game da sace ɗaliban Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke ƙaramar Hukumar Kankara a Jihar Katsina.
Adams ya ce rashin hankali ne ƴan fashi suka sace sama da ɗaliban makarantar sakandare 600 a lokacin ziyarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a jihar Katsina.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan naɗa shi a matsayin Manzo a ma’aikatun ceton a ranar Lahadin da ta gabata a jihar Legas, Adams ya zargi gwamnatin Shugaba Buhari da laifin matsalar tsaro a Najeriya.
“Ba za a iya musun gaskiyar cewa Nijeriya na kan mararraba ba saboda halin da ƙasar ke ciki a yanzu manuniya ce kan cewa wannan gwamnatin ta gaza,” in ji Adams.
“Ta yaya za ku iya bayanin sace ɗaliban kimanin 600 a wata makaranta? Abin takaici ne yarda da wannan a matsayin iyaye, amma kuma abin dariya ne a matsayin shugaba wanda ya san abubuwa da yawa game da abin da ake buƙata don jagorantar ƙasa kamar Najeriya.
“Satar ta faru ne a jihar Katsina, mahaifar shugaban ƙasar, inda yanzu haka ya ke ziyarar mako guda. Wauta ce.
“Dukkanin taron hujja ne na gazawar gwamnati mai ci a yanzu a ƙarkashin Buhari kuma Najeriya na cikin doguwar yaki da masu tayar da ƙayar baya.”
A halin da ake ciki, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, a ranar Lahadi ya bayyana cewa ɗalibai 333 sun ɓata biyo bayan harin da ƴan bindiga suka kai a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Kankara, a safiyar ranar Asabar.