Rashin Shugabanci na Gari ke kawo ta’addanci A jihohin Arewa maso Yamma ~Cewar Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce rashin shugabanci na da alakar kai tsaye” kan yawaitar ‘yan fashi da garkuwa da mutane a shiyyar arewa maso yamma.
Shettima ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar hadin kan ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adanai, da noma na jihohin Arewa, CONSCCIMA, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shugaban kungiyar Dalhatu Abubakar ne ya jagoranci kungiyar.
Arewa maso yamma ta ƙunshi jihohi bakwai: Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, da Zamfara.
Musamman jihohin Zamfara, Katsina da Sokoto sun kasance wuraren da ‘yan fashin suka addabi jama’a, lamarin da ya janyo sace mutane da kashe-kashe a ‘yan kwanakin nan.
Shettima ya ce masu ruwa da tsaki a yankin arewa baki daya “dole ne su koma kan hukumar zana zane, su sake duba yadda al’amuran yankin suke, sannan su fito da kwararan matakai na sake farfado da al’ummarmu.
Shettima ya ce, “Yana da matukar muhimmanci ga arewa ta fara shirin sake fasalin yankin da kuma sake farfado da shi don sake mayar da shi domin a samu ci gaba cikin sauri,” in ji Shettima.
“Yawancin batutuwan da shugaban CONSCCIMA ya bayyana suna da matukar tayar da hankali, domin wadannan batutuwa ne da suka shafi rayuwa da jin dadin jama’armu.
“Ba za a taba samun ci gaba ba tare da zaman lafiya ba, kuma ba za a taba samun zaman lafiya ba sai da ci gaba