Addini

Rashin Tsari ne Ya Jefa Makarantun Allo A Matsala Inji Shekarau

Spread the love

Rashin Tsarin ne Ya Jefa Makarantun Allo Acikin Matsala, A cewar Mal.shekarau

Daga Abdulrashid Abdullahi,Kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa rashin yin kyakkyawan tsari ne ya haifar da halin da makarantun allo suke ciki.
Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ya ce ya ji wani Gwamna daga Arewacin Nijeriya na cewa wai makarantun allon nan ba su tsinana wa kowa komai ba.

Shekarau, ya ci gaba da bayar da amsa cewa ba domin wannan makarantun allon da aka yi tsawon shekaru daruruwa ba da shi wannan Gwamnan na Arewa da bai iya karanta fatiha ba.

“Tsari ne na shekaru da yawa daruruwa da aka yi saboda haka ba zai yiwu ba wani ko wasu su zo lokaci daya su ce za su rusa wannan tsarin ba sai dai a hankali kuma sai an yi wa tsarin wani ingantaccen tsari tukuna.

Ya ce ” a lokacin da nake Gwamnan Kano hakika na fahimci abubuwa da yawa game da tsarin makarantun allo kuma na yi tsare-tsare da dama domin inganta tsarin na kuma samu nasara kwarai”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button