RAWA A GABAN MAZAJEN AURE BA HARAMUN BANE
WANNAN SUNNAR ANNABI MUHAMMADU S.A.W CE FA
Manyan matan Masu kudi ke tikar rawa a gaban mazajensu haka alamunsu ya nunamin dommin nasan ba matan talakawa bane daganin alamarsu
Naji Sai surutu akeyi cewa basuyi daidai ba kuma ana zaginsu da cewa
‘Yan iskane matan sun aikata badala
To ni anawa ra’ayin da ‘yan hujjojin da nake dasu a addini wannan ba wani abu bane face dabi’a mai kyau ta raya sunnar Annabi s.a.w
ga matan auren
kuma da’ace matan aure zasu dage Kullum sunayin haka ga mazajensu na tabbatar da maza sun rage zaman Majalisa neman mata banza tare yawan fada ce fadace Tsakanin ma’auratan
kuma hakan zai kawo karshen yawan rabuwar aure,
nasan wasu zasu yarda dani kuma zasuce hakane nayi maganar gaskiya,
haka zalika kuma wasu zasuyi tambaya kamar haka suce M inuwa amma matsalar da Kuskuren shine yadda suke saka Bidiyon a social media kowa yana gani
Ni kuma sai nace daku a addini Ai akwai hadisin urfi ko? kuma shi urfi yana canjawa daidai da zamani don hakan idan wannan Bidiyon da matan aure suke sakawa a social media zai iya kawo gyaruwar auren wasu kuma ya zama abin koyi a garesu
To hakika wannan babu laifi idan har da yardar mazajensu suke saka wannan Bidiyon a social media wannan ba wani laifi bane a addini Islam idan hakan na iya saka mazajen nasu farin ciki to hakika wa’yan nan mata na iya shiga aljannah ta hanyar wannan Bidiyon domin kai tsaye babu wani Hadisi da yace karku saka Bidiyon Soyayyar ma’aurata a social media…
Social media ta koya mana abubuwa da dama social media ta taimakemu a addinance kuma taimako mai girma don haka ba ko wanne abu bane idan mun gani a social media zamu rinka kushewa muna 6atawa kai tsaye hakika yana da kyau murinka duba Alkhairi kafin duba izuwa sharrinsa…
Ra’ayin na ne…