Labarai

Rayuwa Bil’adama ta rasa kimarta a karkashin Mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ~NEF

Spread the love

Wata Kungiya ta NEF tayi wannan bayanin ne a matsayin martani ga mummunan harin da ya yi sanadin mutuwar manoma shinkafa 40 a yankin Zabarmari na jihar Borno a ranar Asabar da ta gabata.
Kungiyar ta kuma bayyana a matsayin ainihin barazanar da ake fuskanta ga noma a Arewacin Najeriya.
Daraktan yada labarai na NEF, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ne ya yi wannan bayanin a cikin wata sanarwa a daren Talata bayan kashe-kashen baya-bayan nan da aka yi wa manoma 43 a Borno cibiyar rikicin Boko Haram.

A cewarsa, “A karkashin wannan gwamnatin, rayuwa ta rasa kimarta, kuma da yawan‘ yan kasa da ke shigowa karkashin tasirin masu laifi. Ba mu ga wata shaida ta nuna yarda daga Shugaba Buhari don girmama rantsuwar da ya yi na samar da tsaro ga ’yan Najeriya ba. A cikin kasashe masu wayewa, shugabannin da suka gaza sosai wajan samar da tsaro zasu yi abin girmamawa su yi murabus.

“Kungiyar dattawan Arewa ta bi sahun‘ yan Najeriya wajen nuna bacin ransu game da kashe-kashen da ake yi wa manoma a jihar Barno da sauran mutane da yawa a kullum a yawancin sassan Arewa. Muryoyinmu sun kasance ba tare da tsayawa ba na dogon lokaci game da matsalar rashin tsaro da ta mamaye yankinmu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button