Labarai

Rayuwa Mai Albarka A Yau Sanata Uba Sani Ya Cika Shekaru Hamisin 50 A duniya.

A Shekarunsa Hamisin 50 ga kadan daga Tarihin sa da Kuma kadan daga gudunmawar sa ga Al’umma, Shin ko kun San waye Sanata Uba Sani?

A takaice Shine Sanata maici yanzu Haka a Majalisar dattijan tarayyar najeriya daga gundumar tsakiyar jihar kaduna.

Ya Shiga  ofishi a 2019 Ya karbi kujerar daga Sanata Shehu Sani.

An Haifeshi a karamar hukumar Zaria ta jihar kadunan Nageriya a Ranar 31 Disamba 1970 yanzu  Yana da Shekaru 50 a Duniya.

Jam’iyyarsa ta siyasa Jam’iyyar All Progressive Congress APC)

Daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, da Jami’ar Ibadan. Sana’a Injiniya, Kuma dan Siyasa Laƙabi (s) Abokin Malam

GA CIKAKKEN TARIHIN…

Rayuwa ta Farko An haifi Uba Sani a ranar 31 ga watan Disamba, 1970, a karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna. Bayan ya kammala karatunsa na farko da na sakandare, ya tafi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna inda ya karanci aikin injiniya na kanikanci wanda ya kammala da babbar difloma ta kasa (HND) da kuma jami’ar Abuja don karatun difloma a fannin kasuwanci sannan kuma ya yi digiri na biyu a fannin kudi. A Jami’ar Calabar Dake Jihar Kuros Riba, Nijeriya.

FANNIN SIYASA.

Sanata Uba Sani ya shiga siyasa bayan dawowar Dimokradiyya a Najeriya a Shekara ta alif 1999, kuma ya goyi bayan dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar people Democratic Party, PDP Cif Olusegun Obasanjo. Bayan lashe zaben shugaban kasa, an nada Uba Sani mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin jama’a. 

Daga baya ya yi aiki a ma’aikatar tarayya ta FCT kan wasu shawarwari da kuma Ma’aikatar Gidaje da Ayyuka ta Jihar Kaduna. 

A shekarar 2011, Sanata Uba Sani ya tsaya takarar fidda gwani na takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya amma Alhaji Hamisu Abubakar ya kayar da shi, 

sannan a 2015, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad el-Rufai ya nada shi a matsayin Mataimaki na Musamman kan siyasa da Al’amuran Gwamnati. Duk da haka, a 2019, Sani ya nuna sha’awarsa kuma ya sake tsayawa takarar Zama sanatan Kaduna ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar siyasa mai mulki, All Progressives Congress, APC kuma an zabe shi Sanata a lokacin babban zaben watan Fabrairun 2019 na Najeriya. Wanda yanzu Haka shine sanatan kaduna ta tsakiya.

KADAN DAGA CIKIN GUDUNMAWAR SA GA AL’UMMA.

A  Shekarar da ta gabata ya dauki nauyin biyama hazikan dalibai kudin jabarawar WAEC da kuma NECO. Wanda kuma ana sa ran cewa zai dauki nauyin karantun su nagaba da sakandari din, Cikin Jerin Makarantun da sanatan ya dauki nauyi sune kamar haka….

 A. KARAMAR HUKUMAR KAJURU 1.

1. Makarantar Kimiyya (Government Technical College) Dake Kajuru

2. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Day Secondary School) Dake kufana

3. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Day Secondary School) dake ldon

4. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Day Secondary School) Dake  kasuwa magani.

 5. Makarantar Gwamnati  Sakandiri (Government Day Secondary School) Dake Maro.

SAI KUMA KARAMAR HIKUMAR KADUNA TA AREWA.

1 Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Girls Secondary School) tafawa Balewa Dake kabala.

2 Makarantar Sakandiri din Mata  (Dalet Girls Secondary School) dake kawo.

3 Makarantar Dr Ahmed Muhammad Makarfi Dake  Hayin Banki. 

4 Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Secondary School) Dake Unguwan Sarki.

5 Makarantar Sakandiri ta Sardaunan Memorial Secondary School, Dake smc unguwan dosa.

SAI KUMA KARAMAR HUKUMAR 

CHIKUN 

1 Makarantar Gwamnati Sakandiri  (Government Secondary School) Dake Gwagwada. 

2. Makarantar Gwamnati Sakandiri  )Government Day Secondary School) Dake Buruku. 

3. Makarantar Sakandiri  (Government Day Secondary School) dake Narayi.

4. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Secondary School,) Dake Sabon Tasha. 

5. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Day Secondary School) Dake Kujama.

KARAMAR HUKUMAR KADUNA TA KUDU

Yakin T Wada 

1. Makarantar Sakandiri ta Mata (Government Girls Secondary School. Dake U/MA’AZU (DAY BOLA)

2. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Day Secondary School) Dake T/NUPAWA

Yankin Unguwar Sunusi  

1. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Girls Secondary School) Dake MAIMUNA GWARZO.

2. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Day Secondary School) Dake KARGI ROAD.

Yankin Makera

1. Makarantar Gwamnati Sakandiri G

(Government Day Secondary School) dake BARNAWA

2. SAI QUEEN AMINA COLLEGE

E.KARAMAR HUKUMAR GIWA 

1. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Secondary School) dake Giwa.

2. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Secondary School) dake Shika.

3. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Secondary School( Dake Gangara

4. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Secondary School( Dake yakawada.

5.makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Secondary School) dake Fatika.

KARAMAR HUKUMAR IGABI LOCAL GOVERNMENT

1 Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Day Secondary School) Dake Jaji

2.  Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Day Secondary School) Dake Turunku.

3. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Day Secondary School) dake Rigachikun 

4. Makarantar Sakandiri (Government Day Secondary School) dake Birnin yaro)

5. Makarantar Gwamnati Sakandiri ( Government Secondary School) dake Makarfi Road Rigasa

6. Makarantar Gwamnati ta Sakandiri dake  Zangon Aya.

G. KARAMAR HUKUMAR BIRNIN GWARI.

1.  Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Secondary School) Dake B/GWARI.

2. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Secondary School) 

Dake RANDAGI.

3. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Secondary School) Dake KAKANGI.

4. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Secondary School, Dake KUYELLO 

5. Makarantar Gwamnati Sakandiri (Government Secondary School) dake DOGON DAWA…

FANNIN DOGARO DA KAI GA MATASA.

Sanata Uba Sani Zai Samawa Manoma Mutun dubu 1,000 MILYOYIN kudi Wanda tuni Yanzu ya fara da mutun Dari 100 kowa Cikin su ya samu Milyan Daya Daya 1m domin dogara da Kai.

Sanata Uba Sani mai wakiltar kaduna ta tsakiya a majalisar Dattijan Nageriya tare da Hadin Kan Gidauniyarsa ta  Uba Sani Foundation da Kwalejin Aikin Noma da Kimiyyar Dabbobi (College Of Agriculture and animal Science) dake  Mando kaduna, sun hada karfi da karfe sun bawa matasa mutun dari 100 Horo Cikin mutun Dubu 1000 da Sanatan yayi alkawarin Daukar nauyinsu domin koya masu hanyoyin sanin dabarun dogaro da kai a Amfanoni da dama tuni matasan kowa ya samu kasonsa.

a karon farko dai an koyawa matasan Kasuwancin kiwon Kifi da kiwon kaji a kwalejin ta Noma,  haka zalika kuma Sanatan be tsaya anan ba harsai da ya tabbatar ya nemawa matasan lamuni daga babban bankin Nageriya CBN domin samun Makudan kudin da zasu fara aikin da aka koya masu kai tsaye…

FANNIN CIGABAN AL’UMMA DA MORIYAR GOBENMU.

Tsawon Zaman sa a Majalisar dattijan Nageriya sanata Uba Sani Ya kai kudri (BILL) na kafa makarantar Kwaleji FCE a karamar hukumar  Giwa.

Samar da kudrin (BILL akan kafa asibitin gwamnatin tarayya a rigasa.

Kudirin (BIL) na kafa makarantan kimiyya gandun daji a Birnin Gwari.

Kudrin (BILL) domin chanja  Polytechnic Zuwa  Makarantan kimiyya ta tarayya.

Kudrin BILL) domin kare hakking kana nan yara

Sai Bill Kan koyarda Ilimin na’ura Mai kwakwalwa da hanyar sadarwa ta zamani

Sai kudrin gyara tsarin babban bankin Nageriya Central bank.

Sanata Uba Sani bayan hawansa  Mulki ya Kafa Ofisoshi takwas 8 Cikin kananan hukumomi bakwai 8 dayake wakilta duk domin jin koken jam’arsa Haka Kuma sanatan ya dauki matasa da dama suna aiki a karkashin sa Wanda yanzu Haka yake biyansu Albashi da kansa.

Barka da Zagayowar Ranar haihuwa Malam Uba Sani.. #US50

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button