Rayuwa Mai Albarka wata Mai Zuwa Sanata Uba Sani Zai Cika Shekaru Hamisin 50 a Duniya.
Shin ko kun San waye Sanata Uba Sani?
A takaice Shine Sanata maici yanzu Haka a Majalisar dattijan tarayyar najeriya daga gundumar tsakiyar jihar kaduna.
Ya Shiga ofishi a 2019 Ya karbi kujerar daga Sanata Shehu Sani.
An Haifeshi a karamar hukumar Zaria ta jihar kadunan Nageriya a Ranar31 Disamba 1970 Yana da Shekaru 49 a Duniya.
Jam’iyyarsa ta siyasa Jam’iyyar All Progressive Congress APC)
Daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, da Jami’ar Ibadan. Sana’a Injiniya, Kuma dan Siyasa Laƙabi (s) Abokin Malam
GA CIKAKKEN TARIHIN…
Rayuwa ta Farko An haifi Uba Sani a ranar 31 ga watan Disamba, 1970, a karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna. Bayan ya kammala karatunsa na farko da na sakandare, ya tafi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna inda ya karanci aikin injiniya na kanikanci wanda ya kammala da babbar difloma ta kasa (HND) da kuma jami’ar Abuja don karatun difloma a fannin kasuwanci sannan kuma ya yi digiri na biyu a fannin kudi. A Jami’ar Calabar Dake Jihar Kuros Riba, Nijeriya.
FANNIN SIYASA.
Sani ya shiga siyasa bayan dawowar Dimokradiyya a Najeriya a Shekara ta alif 1999, kuma ya goyi bayan dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar people Democratic Party, PDP Cif Olusegun Obasanjo. Bayan lashe zaben shugaban kasa, an nada Uba Sani mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin jama’a. Daga baya ya yi aiki a ma’aikatar tarayya ta FCT kan wasu shawarwari da kuma Ma’aikatar Gidaje da Ayyuka na Jihar Kaduna.
A shekarar 2011, Sanata Uba Sani ya tsaya takarar fidda gwani na dan takarar sanata na Kaduna ta Tsakiya amma Alhaji Hamisu Abubakar ya kayar da shi, sannan a 2015, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad el-Rufai ya nada shi a matsayin Mataimaki na Musamman kan siyasa da Al’amuran Gwamnati. Duk da haka, a 2019, Sani ya nuna sha’awarsa kuma ya sake tsayawa takarar sanata na Kaduna ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar siyasa mai mulki, All Progressives Congress, APC kuma an zabe shi Sanata a lokacin babban zaben watan Fabrairun 2019 na Najeriya.