Labarai

Rayuwar Balarabe Musa Ta ban mamaki ce ~Sanata Uba Sani.

Spread the love

Sanatan kaduna ta tsakiya Malam Uba Sani ya Girgiza da Rasuwar tsohon Gwamnan jihar kaduna balarabe Musa inda Cikin Alhini ya rubuta a shafinsa na Twitter Yana cewa Tare da asara Mai zurfin amma na mika wuya ga nufin Allah Madaukakin Sarki na samu labarin tafiya ta har’abada na ɗaya daga manyan Cikin ‘yan siyasar Najeriya kuma mai kare muradun talakawa, Mai Kima Alhaji Balarabe Musa , tsohon gwamnan jihar kaduna.


Sanatan Yace Balarabe Musa ya kasance mai iya magana Mai nuni da zamani Rayuwarsa ta ban mamaki tana da alaƙa da haɓakawa da kare haƙƙoƙin marasa ƙarfi da marasa galihu, yaƙi da ikon mulkin soja, da ba da shawarwari game da haƙƙoƙin asali da ‘yanci, da faɗin gaskiya kan iko. Ya kasance mara tsoro da daidaito.


Lallai Najeriya ta yi rashin ɗayan Dan Kasa Mai daraja. Ya yi fice ta fuskoki da dama: ɗan ƙasa, ɗan siyasa na gaba gaba mai sharhi kan al’amuran jama’a, mai kula da rubutu, mashahurin akawu, mai taimakon jama’a da ɗan adam. Zanyi kewarsa sosai.


Ina mika ta’aziyyata ga Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai da Shugaba Muhammadu Buhari kan rasuwar wannan babban dan Najeriya. Ina Ta’aziya ga Mallam Sagir Balarabe da ilahirin dangin Balarabe Musa. Da fatan Samun hakurin jure rashinsa dukda cewa Rashin Alhaji Balarabe Musa ya shafi rayuka da yawa wa’yanda da baza’a iya ambatar su ba. Lallai zai kasance a cikin zukatan mutane da yawa…


Allah Ta’ala Ya gafarta wa Alhaji Balarabe Musa kurakuransa Ya kuma ba shi hutu na har abada. Amin. 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button