Lafiya

Rigakafi : Aikace – Aikace Tareda Yawan Motsa Jiki Na Bada Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Covid – 19 — Masana.

Daga Miftahu Ahmad Panda.

A daidai Wannan Kadami da masu Dauke da Annobar Wannan Cuta ta Covid – 19 yahaura Dubu Goma a Fadin Kasarnan, Kwararren Farfesan nan na Bangaren Kashi Kuma Daraktan, “Motsa Jiki Shine Magani a Najeriya”, Dr. Ade Fatai Adeniyi, Yabayyana Dangantakar datake Tsakanin Aikace – Aikace Tareda Yawan Motsa Jiki Daga Kamuwa Da Cutar Covid – 19.

A takardar da Farfesan ya Gabatar Mai taken ” Cigaba Da Motsa Jiki a Lokacin Wannan Annoba ta Covid – 19 : Mataki Bayan Mataki “, Farfesa Adeniyi ya Bayyana cewar Hakika Motsa Jiki Daga Lokaci Zuwa Lokaci yana Kare Mutum Daga Kamuwa Da cututtuka Iri Daban – Daban Domin Kuwa a Duk Lokacin da kake Motsa Jiki to Babu Shakka Kana Karawa Garkuwar Jikinka Karfine Domin Ganin ta yaki Dukkannin wata Cuta da take kokarin Shiga Jikin Dan Adam.

Haka Zalika Farfesan yakara da Cewar Yawan Motsa Jiki zai Taimaka maka Don Ganin Ka rayu Cikin Koshin Lafiya.

Sharshin Mikiya A Takaice : Tabbas Motsa Jiki Abune Muhimmi da Dukkannin Wanda Ya rungumeshi zaiga cigaba a Cikin Lamuran Kasancewarsa Lafiya, Haka Zalika Zai samu Dumbin Kariya Daga Dubban Cututtukan da Suke kama Al’umma Suna Hanasu Samun Kwanciyar Hankali da Natsuwa.

Bawai Iya Kwallon Kaface Motsa Jiki ba, A’a Dukkannin Wani Aiki, Gudu, Tsalle da Makamantansu da zakayi Matukar Gumi Zai Tsatstsafo daga Jikinka to Sunansa Motsa Jiki.

👆Wannan Shine Rigakafin Cutar Covid – 19 Mafi Sauki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button