Labarai

Rikicin Mali:- Osinbajo yya Halarci Taron Koli Na ECOWAS A Ghana.

Spread the love

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya tashi daga Abuja a yau Talata zuwa Accra babban birnin Ghana, don halartar wani Babban taron koli na kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, kan halin da ake ciki a Mali.

Kakakin Mista Osinbajo, Laolu Akande, a cikin wata sanarwa ya ce mataimakin shugaban kasar ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari ne a taron.

Osinbajo zai bi sahun sauran shugabannin yankin domin tattauna rikicin siyasa a Mali da kuma matsalar tsaro a yankin baki daya.

Taron na Accra zai kasance wani bangare na kokarin da shugabanni da dama ke yi a yankin don warware rikicin Mali.

Yayinda yake a Accra, mataimakin shugaban kasar zai kuma hadu da wakilan al’ummar Najeriya a Ghana domin tattaunawa kan matsalolin da ke damun su a kasar ta Afirka ta Yamma.

Osinbajo yana tare da Ministan tare da Ministan Harkokin Wajen kasashen Waje, Amb Zubairu Dada.

Ana sa ran mataimakin shugaban zai dawo Abuja a yammacin yau Talata.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button