Rikincin Ibadan A matsayina na minista Musilmi Dan Arewa na yi magana da gwamnan Oyo ~Dr Pantami
Muna jajantawa yan’uwa da suke Jahar Oyo da sauran jihohin kudu, wadanda suka rasa rayukansu Allah ya jikansu, wadanda suka rasa dukiyoyi Allah ya mayar musu da Alkhairi, wadanda suke cutar da mu Allah ya kunyatar dasu. Muna rokon Allah “Alhayyu Al Qayyum” da ya kawo masu Dauki.
Nayi kokarin Kiran Gwamnan jihar Oyo ban samu damar magana da shi ba, Amma na samu magana da Deputy Governor na Garin Oyo, na Nuna masa damuwa da duk kalar rashin jin dadi a matsayina na Dan Nigeria Kuma Dan Arewa Musulmi, ya fadamin matakai da ake dauka Kuma ya bani wasu muhimman bayanai game da Rikicin.
Na Kira Gwamnan Lagos (Sanwo Olu) da ke shima na san irin kokarin da yake yi Akan irin wadannan abubuwa, na Fada masa irin takaicin da Yan Arewa suke ciki.
Munyi musayar saƙonni da gwamnan Ikiti akan Rikicin.
Na Kira abokin aikina wato Minister na ‘Yan sanda yake fadamin irin mataki da suke dauka Akan abun, suna waya da Commiisoner of Police na Garin yana bibiyar halin da suke ciki. Kuma yance an kai musu taimako na Gaggawa ga wadanda suke can.
Gwamnan Lagos da nake gaya masa har yanzu abun Bai kare ba, na samu wasu Video clips daga wasu Yan uwa matasa yake cewa a tura masa Ya gani.
Shi Kuma Minister na Yan Sanda yace in akwai wasu location da suke da problem a bashi.
Na Kira shugaban Gwamnonin Arewa wato Gomnan Plateau akan matsalar a matsayinsa na shugaban Gwamnonin Arewa Kuma yan Arewa ake kaiwa hari, wajibi ne yayi magana akai. Hakuri yana da iyaka idan hakurin mutum ya kare babu dadi.
Wadanda muke shawara dasu akan abun irinsu Prof. Zulum tun jiya muke shawara dasu akan yanda za’a Kai doki da samo solution akan rikicin.
Bama bukatar sai an fito fili ana fadan irin kokarin da muke akan irin wadannan rikicin, yardar Allah muke nema. Allah Yana sheda idan irin wannan matsalar ya taso, Ina waya da akalla mutum 30 da abun ya shafa saboda magance matsalar.
Doka ta Nigeria, kowani Dan kasa yana da damar ya zauna a inda yake so ya zauna, idan yayi laifi sai a kaishi kotu a hukuntashi.
ubangiji Allah ya kawomana karshensa wannan fitina ya zaunar mana da kasar mu lpya,