Siyasa
Rikita Rikitar Siyasa Ta Sa Jam’iyyar APC Ta Dakatar Da Mai Taimakawa Buhari Kuma Surukin Tinubu.
Yayin da Rikici ya zurfafa, Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar All Progressives Congress APC a jihar Ekiti, rikicin da yake ta kara kamari, hakan ne yasa jam’iyyar ta dakatar da shugabannin jam’iyyar 12 kwanan nan.
Majiyarmu ta gano cewa da mai baiwa Shugaban kasa shawara, Sanata Babafemi Ojudu; siriki ga Sanata Bola Tinubu, da Oyetunde Ojo; da tsohon dan takarar gwamna, Dr Wole Oluyede; da Ayo Ajibade; da Femi Adeleye, da Cif Akin Akomolafe; da Bamigboye Adegoroye; da Olusoga Owoeye; da Dele Afolabi; da Toyin Oluwasola da Bunmi Ogunleye duk jam’iyyar ta dakatar da su.
Bayanin dakatarwar yana kunshe ne a cikin wata wasika da Sakataren Yada Labaran APC na jihar Ekiti, Ade Ajayi ya sanya wa hannu wanda a ranar Alhamis.