Labarai

Rundunar Sojan Nageriya ta fitar da Jerin sunayen ‘yan Boko Haram da suke nema ruwa a jallo

Spread the love

Rundunar Sojin Najeriya ta fitar da jerin sunayen mutane 86 da take nema dangane da ayyukan ta’addanci. Ana zargin wadanda ke cikin jerin sunayen ‘yan kungiyar ta Boko Haram. A Sakin na baya-bayan nan shi ne na hudu da hukumomin soja suka fitar, wadanda a baya suka fitar da jerin sunayen ‘yan ta’addan da ake nema.

Tukur Buratai, shugaban hafsin soji ne ya kaddamar da jerin sunayen tare da Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, a babban sansanin sojojin Najeriya, Chabbal da ke karamar hukumar Konduga a Borno.

Buratai ya ce wadannan taruka guda biyu na daga cikin ayyukan da aka tsara don tunkarar kawo karshen ayyukan Boko Haram a yankin Arewa-maso-Gabas.

Babban hafsan sojan ya ce babu wani “yara CJTF” da zai shiga cikin wannan aiki, yana mai kira ga jama’a da su tallafawa sojoji wajen kamo ragowar maharan.

Fitacce a cikin jerin sunayen shine shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, wanda aka ayyana ya mutu a wasu lokuta a baya.

Sauran sun hada da Abu Musa Al Barnawi, Modu Sulum, Malkam Umar, Bello Husba, Yan Kolo, Ibrahim Abu Maryam, Baka Kwasari, Bana Gonna, Mohammed Abu Maryam, Abu Imma, da Abu Dardda. Da sauransu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button