Tsaro

Rundunar Sojin Sama Zata Aike Da Jiragen Yaki Tare Da Dakaru Na Masamman Jihar Gombe

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Rundunar Sojin saman Najeriya ta shirya aikewa da jirgin yaki, tare da wasu dakaru na musamman zuwa jihar Gombe, domin magance matsalar tsaro da ayyukan ‘yan ta’adda A Jihar.

Shugaban Hafsin Sojojin Saman na kasa Sadique Abubakar, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya a hedkwatar hukumar dake Abuja.

A rahoton da mai magana da yawun hukumar ya fitar Ibikunle Daramola ya bayyana cewa rundunar za tai aike da dakaru na musamman da jirgin yaki jihar domin magance matsalar tsaro haka zalika rundanar zatai aiki tukuru domin magance matsalolin tsaro da ya addabi yan kunan Arewa maso gabashin Najeriya.

Rundunar ta kuma godewa gwamnan bisa fili da gwamnatin jihar ta bayar dan gina sansanin sojin a jihar.

Haka zalika Hafsin Rundunar Abubakar ya tabbatar da cewa rundunar zata aike da dakarun nan da kwanaki biyu masu zuwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button